150115-kungiyar-kasar-sin-ta-lashe-kofin-ITTF-bello.m4a
|
'Yan wasan kasar Sin Zhang Jike, Fan Zhendong da Xu Xin dukkansu sun lashe takwarorinsu na kasar Austria da ci 3 da nema, wanda hakan ta baiwa Sin damar kare kambinta. A nata bangaren, kasar Austria ta zamo ta 2 a teburin gasar, sakamakon da ya kasance mafi kyau da kasar ta taba samu a wannan gasa ta cin kofin ITTF.
A wasannin da suka gudana tsakanin mutane dai dai, dan wasan kasar Sin Fan Zhendong ya lashe Daniel Habesohn da ci 3 da nema, yayin da Zhang Jike shi ma ya lashe Robert Gardos da ci 3 da ba ko daya. Haka zalika a wasan da ya gudana tsakanin 'yan wasa biyu-biyu, Zhang da Xu sun lashe 'yan wasan Austria Stefan Fegerl da Habesohn da ci 3 da nema.
A karshe dai, kungiyar kasar Sin ta dauki wannan kofi tare da kyautar kudi da yawansa ya kai dalar Amurka 50,000, yayin da kungiyar Austria ta samu dala 25,000.
A wani labarin mai alaka da wannan batu kuma, dan wasa Aruna Quadri, haifaffen jihar Oyo ta tarayyar Najeriya, wanda ke buga kwallon Ping Pang a kasar Potugal, ya samu lambobin yabo na fitaccen dan wasan kwallon tebur na shekarar 2014, da kuma tauraron hukumar kwallon tebur ta kasa da kasa na wannan shekara, lambobin da dan wasan ya karba a 'yan kwanakin baya a birnin Dubai.
An dai zabi Quadri daga cikin kwararrun 'yan wasan kasashen daban daban, ciki hadda Fan Zhendong, da Xu Xin na kasar Sin, da Marcos Freitas na kasar Portugal.
A cewar ITTF, dalilin da ya sa aka ba Quadri lambobin shi ne, domin yaba masa kan yadda ya samu ci gaba sosai a teburin manyan wasannin kwallon tebur na duniya a shekarar 2014, ta yadda ya zama dan wasa dan asalin Afirka da ya fi samun ci gaba a wannan fanni.(Bello Wang)