Shugaban Faranasa ya samu tarbo a filin jiragen saman kasa da kasa na Hamani Diori dake Niamey daga takwaransa na kasar Nijar Mahamadou Issoufou tare da manyan shugabannin hukumomin kasar, manyan jami'an gwamnati, sojoji da fararen hula, jakadun kasashen waje dake kasar da kuma jama'a.
Bisa tsawon hanya ta kusan kilomita 20 dake kawai zuwa fadar shugaban kasa, jama'a ne suka sosai rike da tutocin Nijar da na Faransa domin yi wa shugaban Faransa barka da zuwa.
Wannan ziyara kuma da za ta kai Hollande kasar Chadi, za ta mai da hankali kan batutuwan tsaro a yayin da kasar Faransa ta kaddamar da aikin jibge sojojinta na Barkhane da za su maye gurbin tawagar sojojin Serval domin yaki da kungiyoyin kishin islama dake yankin Sahel.
A yayin wannan ziyara, mista Hollande ya kai ziyara a wurin da wani rukunin sojojin saman Faransa suke sarrafa jiragen marasa matuka dake shawagi kan yankin Sahel musamman ma a arewacin kasar Mali dake iyaka da Nijar da kuma ziyarar wani injin dake samar da ruwa ga birnin Niamey na kamfanin ruwa na SNE, reshen kamfanin Faransa Veolia, da kuma wani sarrafa abincin kananan yara dake kudancin birnin Niamey. (Maman Ada)