Za mu cigaba da tsayawa kasar Mali domin dafawa wannan manufa mai kyau, domin yakin da muke yi, yaki mai daraja, dalilin muna kishin demokaradiya ne, za mu iyakacin kokarin mu domin kawo na mu taimako wajen kawar da ta'addanci a yankin Sahara in ji shugaban kasar Nijar.
Jami'an tsaron mu zasu cigaba da kawo nasu taimako a cikin tawagar MINUSMA, a kasar Mali ko a wani wuri, idan aiki ya kira mu to za mu je in ji Mahamadou Issoufou.
Sojojin Nijar 9 dake cikin rukunin Nijar da aka tura Mali na tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar Mali (MINUSMA) aka kashe a ranar Jumma'a a wani kwantan bauna na wasu mayakan ta'addanci da ba'a tantance su ba, a tazarar kilomita 80 daga garin Menaka dake yankin Gao a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Ansongo a kuriyar arewacin Mali domin daukar kayayyaki.
Tun cikin watan Agusta, aka tura wani rukunin sojan Nijar na biyu dake kunshe da mutane 850 a arewacin Mali.
Nijar da Mali na raba kan iyakar kasa guda bisa tsawon kilomita fiye da 800, kana al'ummomin wurin na amfani da harsuna iri daya wato Tamajek, Songhoi, fulfulde da sauransu. (Maman Ada)