Gwamnatin kasar Nijar, bayan wani zaman taron ministoci a ranar Asabar a fadar shugaban kasa kuma a karkashin jagorancin shugaba Mahamadou Issoufou, ta sanar da aiwatar da zaman makoki na kwanaki uku a dukkan fadin kasar, bayan mutuwar sojojin kasar Nijar tara a wani harin kwantan bauna a arewacin kasar Mali a makon da ya gabata.
Domin martaba mutuwarsu, za'a kaddamar da zaman makoki na kwanaki uku tun daga bakin ranar Lahadi, kana dukkan tutocin kasar za'a sauko su kasa, in ji sanarwar gwamnatin kasar.
Niyyar sojojin kasarmu ita ce ta kare martabobin tsarin demokuradiyya da 'yanci idan wadannan suna fuskantar barazana, to kasar Nijar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a kusa da 'yan uwanta na kasar Mali, in ji sanarwar gwamnatin kasar Nijar. (Maman Ada)