A cikin yarjejeniyar,an amince cewa rassan kamfanonin biyu za su nada 'yan kasar ta Nijar a matsayin Darektoci tsakanin watan Yuni na 2014 zuwa 2016.
Malam Hama Amadou yayi bayanin cewa yanzu haka an dakatar da hakar sinadarin na uranium wanda zai sa kasar ta zama ta biyu a duniya wajen hako wa inda zata samar da tan 5000 duk shekara na sinadarin har sai an samu daidaituwa a kasuwannin duniya.
A dangane da hakan kakakin majalaissar ya zargi kamfanin da daukan matsayin da zai amfana mata ita kadai yana mai cewa dakatar da hakan sinadarin a yanzu haka zai kawo matsalar rashin aikin yi ga matasan kasar da dama.
Ita dai wannan kamfanin hakar ma'adinan ta kasance wadda take hakar sinadarin Uranium a yankin agadez dake arewacin kasar ta hannun rassan ta guda biyu wato Somair da Cominak fiye da shekaru 50 da suka gabata.
(Fatimah Jibril)