in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika 18 suna Nijar domin wani horon soji na hadin gwiwwar yakar ta'addanci
2014-02-21 20:27:38 cri
Kusan sojoji 1000 ne da manyan jami'an soji daga kasashe 18 na nahiyar Afrika suka hallara a Jamhuriyar Nijar domin fara wani horon soji na yakar ta'addanci a yankin sahel.

Horon sojin mai taken 'Flintlock' za'a yi shi ne a garurruwan Agadez,Diffa da Tahoua tsakanin ranakun 20 ga watan nan na fabrairu zuwa 9 ga watan Maris.

Horon na 'Flintlock' dai an kirkiroshi ne a shekara ta 2005 da nufin inganta dabarun kariya da kuma tsaro sannan a habaka cudanya tsakanin kasashe don kare al'ummar kasashen yankin na sahel.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China