Shugaban kasar Faransa Francois Hollande zai jagoranci bukukuwan a karo na 70 na zuwa sojojin kawance a kudancin Faransa tare da shugabanni kusan ashirin da gwamnatocin kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara.
Zuwan sojojin kawance a wannan yanki ya kasance wani aikin soja da aka gudanar a lokacin yakin duniya na biyu daga shekarar 1939 zuwa shekarar 1944) inda daga ranar 15 ga watan Augustan shekarar 1944 sojojin Faransa, Ingila, Amurka da Afrika suka isa kudancin Faransa domin kwato kasar daga hannun sojojin kasar Jamus, lamarin da ya kawo karshen yakin. (Maman Ada)