Yarjejeniyoyi na jimillar kudin Euro fiye da milyan 74, kwatankwacin kudin Sefa biliyan 49, sun shafi fannoni daban daban wadanda suka hada kiwon lafiyar yara, kanana 'yan kasa da shakaru biyar na haihuwa, makamashi tare da fafada layin wutar lantarki na kamfanin wutar lantarki na kasa NIGELEC, fannin ilimi, noma da kiyo a yankuna goma sha daya da aikin gina madatsar ruwa Kandaji ya shafa, da kuma tsaron abinci. Baya ga wannan kuma akwai taimakon kungiyar tarayyar Turai na kusan Sefa biliyan 8.
Francois Hollande ya isa Niamey a ranar Jumma, bayan ya fito daga birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire tare da wata babbar tawagar dake kunshe da manyan 'yan kasuwa. A Niamey, wadannan manyan 'yan kasuwa na Faransa sun yi tattaunawa tare da takwaransu na kasar Nijar. Shugaban kasar Faransa ya bar Niamey a ranar Jumma'a da yamma zuwa birnin N'djamena na kasar Chadi a matsayin zangon karshe na wannan rangadi nasa a Afrika. (Maman Ada)