in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kauyuka 30 za su ci gajiyar wutar lantarki a kasar Nijar
2014-02-02 16:30:23 cri
Gwamnatin kasar Nijar na shirin samar da wutar lantarki nan ba da jimawa ba ga wasu kauyuka 30 na kasar ta hanyar hasken rana da kuma kafa wata tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana, a cewar wata majiya mai tushe a ranar Asabar a birnin Niamey.

Yarjejeniyar samar da kudaden wannan aiki da suka tashi dalar Amurka miliyan 34.54 kimanin Sefa wajen biliyan 16.6, an rattaba hannu kanta a ranar 12 ga watan Satumban shekarar 2013 a birnin New Delhi na kasar Indiya tsakanin gwamnatin kasar Nijar da Exim Bank na kasar Indiya da kuma gwamnatin Nijar ta amince a wannan mako a birnin Niamey.

Mutanen kasar Nijar, musammun dake babban birnin kasar na fama da daukewar wutar lantarki a tsawon shekaru da dama, duk da kokarin da hukumomi da shugabannin kamfanin Nigelec suke yi na daidaita wannan matsala da ma warware ta kwata kwata. Domin fuskantar wannan matsala gwamnatin Nijar ta kafa wani babban shirin samar da wutar lantarki, da ya hada da gina tashar samar da wutar lantarki mai kafin megawatt 100 tare da taimakon bakin BOAD bisa jimillar kudin Sefa biliyan 17, samar da wutar lantarki ta hanyar kwal na Salkadamna dake cikiyar kasar da kuma gina madatsar ruwan Kandadji da za ta samar da wutar lantarki megawatt 130 000 ta yadda wannan zai taimakawa kasar Nijar samun wutar lantarki cikin sauki a wannan shekara. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China