Shugaba Al-Bashir wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru, ya jaddada cewa za a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara a baya. Ya ce duk wani dan jam'iyyar NCP mai mulkin kasar da ya bayyana burin jinkirta zaben, hakan ra'ayi ne na kashin kai, amma ba na jam'iyyar ta NCP ba.
Wasu jam'iyyun adama na kasar Sudan din dai sun yi kira da a jinkirta zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar, don samun karin lokacin shiri da tattara kudin gudanar da zaben, da kokarin kara samun kuri'u.
Kaza lika wadannan jam'iyyu sun bukaci a wargaza gwamnatin kasar mai ci, a kafa gwamnatin wucin gadi domin gudanar da harkokin kasar kafin zaben. Sai dai shugaba Al-Bashir ya yi watsi da wannan bukatu na jam'iyyun adawa. (Zainab)