Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai halarci taron tattaunawar musamman kan goyon bayan kungiyar raya kasashen gabashin Afirka IGAD wajen shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu, wanda za a shirya a tsakanin bangarori masu gwagwarmaya da juna a Sudan ta Kudu tare da taimakon kungiyar IGAD a birnin Khartoum, hedkwatar kasar Sudan a ranar 12 ga wata a yayin da mista Wang ke ziyarar aiki a kasar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya sanar da hakan a ranar yau Lahadi 11 ga wata. Inda ya kara da cewa, mahalarta taron za su tattauna kan yadda za a taimaka da kuma goyon bayan kungiyar IGAD wajen kokarin gaggauta tabbatar da samun sulhuntawa a Sudan ta Kudu, ta yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar cikin hanzari. (Tasallah)