Cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a jiya Talata Mr. Ban ya yi Allah wadai da wannan mataki. Har wa yau Mr. Ban ya ce matakin zai haifar da babbar illa ga sha'anin jin kai a kasar Sudan, musamman ma a wannan lokaci da bukatun jin kai a kasar ke karuwa, ake kuma kara fuskantar kalubale a kokarin shawo kan matsalar.
A daya bangaren, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka, da kungiyar EU sun yi tir da wannan mataki da gwamnatin Sudan ta dauka kan jami'an MDDr.
A kwanakin baya ne dai gwamnatin kasar Sudan ta bukaci babban jami'in MDD mai kula da ayyukan jin kai dake kasar Ali Al-Za'tari, da wakilin hukumar shirin raya kasa na MDD dake kasar Yvonne Helle, da su fice daga kasar ta Sudan. (Zainab)