Gwamnatin Somalia da rundunar AMISOM sun ce garin ya fada hannun dakarun ba tare da fuskantar wani gagarumin gumuzu ba daga bangaren mayakan Al-shabaab, wadanda garin ya dade yana karkashin ikonsu.
Gidan Radiyo na Mogadishu ya ruwaito cewa, wani rukuni na dakarun wanzar da zaman lafiya da kuma na kasar ta Somalia sun kwace ikon mulkin garin daga hannun 'yan kungiyar ta Al-Shabaab, kuma a yanzu garin na hannun dakarun kiyaye zaman lafiyar.
Kame garin Barawe wata babbar nasara ce ga dakarun kiyaye zaman lafiya, wanda suka kaddamar da harin da motocin sulke tun watan Satumba da muradin tunkude 'yan tsageran Al-Shabaab daga wuraren da suka yi kaka gida. (Suwaiba)