Kasashen Sin da Somaliya na cin gajiyar dadadar dangantaka ta dogon tarihi. A yanzu haka, Somaliya da Sin, kasashe ne aminai, in ji mista Mohamoud jim kadan bayan ya dawo daga wani rangadin aiki a yankunan da aka karbe daga hannun kungiyar Shebab.
Gwamnatin Sin na samar da kayayyakin jin kai ga Somaliya tun lokacin faduwar gwamnatin tsakiya na Somaliya a shekarar 1991, in ji shugaba Mohamoud.
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Somaliya ya rufe kofa fiye da shekaru ishirin, amma sake bude shi a ranar Lahadin da kuma nada sabon jakada za su taimakawa wajen karfafa huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu, in ji shugaban Somaliya. Matsalar tsaro ta kyautatu a Somaliya, wannan ya kasance lokaci mai kyau domin maido da masu zuba jari na kasashen waje, har ma da kamfanonin kasar Sin, domin zuba jari a bangarori da dama na tattalin arziki in ji shugaba Mohamoud. (Maman Ada)