Kwamitin tsaro na MDD ya amince a lokaci guda da kudurin dake baiwa kasashe mambobi damar sanya ido kan yankunan da zaton suna kunshe da kwal a Somaliya, matakin dake manufar kara karfafa wani haramcin kan hakar kwal da kuma rage karfin wata muhimmiyar hanyar samun kudi ta kungiyar Al-Shebaab. Kudurin ya samu amincewa da kuri'u goma sha uku yayin da kasashen Rasha da Jordaniya suka janye kafa.
Mista Wang Min, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, ya jefa kuri'ar amincewa da kudurin da sunan tawagar kasar Sin.
Kasar Sin na imanin cewa kudurin mai lambar 2182 za'a aiwatar da shi yadda ya kamata kuma kalma na bin kalma, in ji mista Wang, tare da jaddada cewa ya kasance wajibi kasashe mambobi suna amincewa da sharudan 'yancin kasa da kasa da ba da kariya sosai ga 'yanci da moriyar kasashen duniya da kasashen da abin ya shafa.
Wang ya sake jaddada muhimmanci ga kwamitin tsaro na MDD da ya saurari cikin natsuwa ra'ayoyin dukkan bangarori a cikin shawarwarinsa kan kudurin, da kuma girmama bukatun kasashe da kungiyoyin shiyoyyin da abin ya shafa. (Maman Ada)