Wani jami'i a birnin mai suna Ahmed Nor ya bayyana cewa, an kara gano gawawwaki 6 a wurin da bam din ya fashe a ranar 13 ga wata, kafin wannan an gano gawawwaki 14, baki daya harin ya haddasa mutuwar mutane 20 a halin yanzu.
A ranar 13 ga wata, shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya yi Allah wadai da wannan hari, inda ya zargi kungiyar Al-Shabaab da kai wannan hari.
Kana wakilan MDD da kungiyar AU dake kasar Somaliya su ma sun yi tir da harin. (Zainab)