Wani harin da jirgi maras matuki na kasar Amurka ne dai ya hallaka jagoran kungiyar ta Al-Shabaab Ahmed Abdi Gonade a ranar Litinin din makon da ya gabata.
Bayan kusan mako guda da hakan ne kuma kungiyar ta tabbatar da rasuwar shugaban nata, tare da ayyana sunan Ahmed Omar Abu Ubeyda a matsayin sabon jagoranta.
Da yake karin haske game da matakan da gwamnatin kasar ke dauka domin dakile yunkuri da mayakan kungiyar za su yi na daukar fansa, ministan ma'aikatar tsaron kasar Khalif Ahmed Ereg, ya ce dakarun gwamnati za su ci gaba da sanya ido kwarai, musamman ganin yadda bayanan sirri ke nuna aniyar Al-Shabaab din na kaiwa gine-ginen hukuma hare-hare.
Daga nan sai ya yi kira ga al'ummar kasar da su taimaka wajen samar da duk wasu bayanan da za su taimakawa mahukunta wajen tabbatar da tsaro. Kaza lika Ereg ya bukaci mayakan kungiyar ta Al-Shabaab da su rungumi shirin lafiya cikin kwanaki 45, wanda gwamnatin Somaliyar ta tsara, duka dai da nufin kawo karshen tashe-tashen hankula da ake fuskanta a kasar. (Saminu Alhassan)