Sai dai duk da yawan masu zuba jari a wannan bangaren ke cigaba da nuna sha'awar su na noman furanni, samo wassu sabbin kasuwanni mai babbar dama wajen cigaba da samar da furanni mai dorewa wani bangare ne da ba'a iya yi sai da shi a koda yaushe, kuma kasar Sin ta zama babbar cibiya ta kai ingantattun furannin roses.
Babban Manajan kamfanin Pigeon Blooms na Kenya, Eliud Njenga wanda gonar shi ke samar da furannin roses ma kasar Sin yace yanzu suna mai da hankalinsu ne a kan yankin Asia da Sin musamman saboda kasuwannin tarayyar Turai suna da masu takarar sosai kuma karuwar wannan sashen a Kenya ya wuce karfin bukatun kasuwannin tarayyar Turai.
Yace yadda jiragen sama ke jigila kai tsaye tsakanin kasashen biyu ya kara samar da yanayi mai kyau wajen shigar da furannin zuwa kasar Sin daga Kenya.
A shekara ta 2013 kamfanin zirga-zirgarjiragen saman Kenyan Airways na kasar dake gabashin Afrika ta fara jigila kai tsaye zuwa kasar Sin, wani abinda ya kara inganta yanayin ciniki tsakanin kasashen biyu.
Sannan kuma yawan al'umma a Sin da karin bukatun ingantattun furannin ya kara bada dama ga kasar ta Kenya wani sabon abokin ciniki da za'a dogara dasu.