Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri a jiya Alhamis 12 ga wata, inda ya nemi kasashe daban-daban da su dauki matakin da ya dace wajen yanke hanyar samarwa wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi kudi, ciki hadda IS da Al-Nusra, don hana su samun kudi ta hanyoyin yin cinikin man fetur da sumogar kayayyakin gargajiya ba bisa doka ba, da yunkurin neman samun kudin fansa da samun jari da za a zuba.
Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD wanda ke rike da shugabancin kwamitin a wannan karo Mr Liu Jieyi ya jagoranci taron da aka kira a wannan rana. Kudurin da aka bayar ya bayyana matukar rashin jin dadin MDD don ganin IS da AL-Nusra da dai sauran kungiyoyin 'yan ta'addanci suna samun kudi ta hanyar cinikin da suke yi, ciki hadda man fetur, kuma watakila wadanda suke da hannu ciki irin wadannan ciniki za a shigar da su cikin jerin sunayen yi musu takunkumi. Kazalika, kwamitin ya nanata matsayin da ya dauka cewa, kamata ya yi kasashe daban-daban su haramta wa wadanda dake da nasaba da kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi wajen yin amfani da kadarori da dukiyoyinsu.
Ban da haka kuma, kwamitin ya yi tir da laifin yin garkuwa da wadannan kungiyoyin suke yi, tare kuma da neman kasa da kasa da su dauki mataki don ceton mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan kudin fansa ko nuna rangwame a siyasance ba. Haka kuma, kwamitin ya nanata wajibcin hada kai tsakanin kasa da kasa idan aka aikata laifin yin garkuwa da mutane.
Bugu da kari, kwamitin ya yi kira ga kasashe daban-daban da su hana jama'arsu zubawa wadannan kungiyoyin kudi, tare da kalubalantar kasa da kasa da su hana wadannan kungiyoyi wajen amfani da tsarin hada-hadar kudi na duniya. (Amina)