in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da gun-gun 'yan kawancen ta na ci gaba da kai farmaki akan kungiyar Islama a Syria da Iraqi
2014-11-11 17:23:08 cri
Rundunar dakaru ta Amurka da gun-gun 'yan kawance na ci gaba da kai hari akan dakarun kungiyar Islama ta IS a Syria.

A cikin kwanaki hudu da suka wuce sun yi amfani da jiragen yaki dabam dabam ciki har da masu sarrafa kansu kansu, wajen aiwatar da hare-hare kimanin 23 a Syria kamar dai yadda rundunar dakarun Amurka ta bayyana.

Kuma a daidai wanan lokaci Amurkar da kngiyar kawancen sun kai wadansu hare-hare 18 a kasar Iraqi a kan wuraren kungiyar ta ISIS.

Ana dai kai wadannan hare-hare ne domin a hankadar da kungiyar Islamar mai tada kayar baya saboda barazanar da suke yi a Iraqi da kuma yankin na gabas ta tsakiya da duniya baki daya。

Sanarwar ta ce nakasa wuraren da kungiyar Islamar ta mallaka zai dakusar da kuzarin ta na aiwatar da hare-hare.

Kasashen dake kai hare haren sun hada da Amurka, Belgium, Canada Denmark, Faransa, Netherlands, Britaniya, Bahrain, Jordan, Saudi Arabia, da kuma hadaddiyar daular larabawa.(Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China