Kawancen kasa da kasar wanda ya gudanar da wani taron ministoci karo na farko a birnin Brussels, ya amince da bukatar ci gaba da yin hadin gwiwa a wannan fage.
Rahotanni sun bayyana cewa taron ya samu halartar wakilai daga kasashe 60 da suka hada da na Amurka, da kungiyar EU, da Faransa, da Jamus, da Ingila, da Canada, da Masar da dai sauransu. An kuma gabatar da wata hadaddiyar sanarwar bayan taron, wadda ta bayyana kokarin da ake yi na dakile kungiyar ta IS a kasashen Iraki da Syria.
Kaza lika sanarwar ta ce karkashin goyon baya daga kawancen kasa da kasa, sojojin Iraki, da dakarun Kurdawa sun kwato yankunan kasarsu daga hannun mayakan na IS. Kana a sakamakon hadin gwiwar kasashen kawancen, kungiyar IS na fuskantar kalubale a fannonin kudi, da na magoya baya.
A jawabin sa yayin taron, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, ya ce ko da yake a yanzu haka an riga an samu gagarumin ci gaba, amma duk da haka mai yiwuwa ne a kwashe shekaru da dama ana yaki da kungiyar ta IS. Ya ce hare-haren sama da kimanin duba daya da kawancen kasa da kasa ya kaddamar sun rage karfin jagorancin kungiyar ta IS, tare da karfinta na samar da guzuri da kaddamar da hare-hare.
A wani ci gaban kuma a 'yan kwanakin baya shugaba Bashar Assad na kasar Syria ya bayyana wa manema labaru na kasar Faransa cewa, haren-haren sama da kawancen kasashen ke kaiwa mayakan kungiyar IS bai yi wani amfani ba.
Shugaba Bashar ya yi nuni da cewa, yayin da ake kai hare-hare ta sama kan 'yan kungiyar IS, kamata ya yi sojojin kasa da suka san halin da ake ciki a yankin su rika gudanar da ayyukan soja a lokaci guda. A cewarsa rashin daukar wannan mataki ne ya sanya kawancen kasashen, gaza cimma nasara cikin watanni biyu da suka gabata. (Zainab)