in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai iyuwa ne IS ta kashe wani dan Japan da ta yi garkuwa da shi
2015-01-25 17:24:04 cri
Bisa wani sabon bidiyon da aka samu a ran 24 ga wata, ya nuna cewa, mai iyuwa ne an kashe dan Japan Haruna Yukawa, daya daga cikin mutane biyu 'yan kasar Japan da kungiyar ta yi garkuwa da su, haka kuma, kungiyar IS ta bukaci da a saki wata mace 'yar kungiyar dake da hannu cikin harin kunar bakin wake.

A yau Lahadi 25 ga wata da safe, firaministan kasar Japan Abe Shinzo ya bayyana cewa, mai iyuwa ne bidiyon da aka samu yana da sahihanci. Kana, ya bukaci da a saki dayan dan jaridar kasar Kenji Goto ba tare da bata lokaci ba, haka kuma cikin wata sanarwar da ya fitar a safiyar ranar 25 ga wata, ya ce, gwamnatin kasar Japan ba za ta ba da kai a gaban kungiyar ta'addanci ba.

Bugu da kari, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ba da wata sanarwa a ran 24 ga wata, inda ya zargi kungiyar IS da kashe dan kasar Japan da ta yi garkuwa da shi, tare da sake yin kira ga kungiyar da ta saki dayan dan jaridar kasar Japan da ta yi garkuwa da shi da ma sauran mutanen da take garkuwa da su ba tare da bata lokaci ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China