in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da kawancenta na ci gaba da hare hare ta sama kan IS a Syria da Iraki
2015-02-02 10:42:14 cri

Sojojin Amurka da kasashen abokanta sun kai hare hare ta sama sau 33 kan dakarun kungiyar IS a Syria da Iraki a tsawon kwanaki biyu na baya bayan nan, in ji ma'aikatar tsaron Amurka a ranar Lahadi.

A cewar sanarwar Pentagone, an kai hare hare ta sama har sau bakwai kusa da Kobane da Ar-Raqqah dake kasar Syria, da suka lalata wani yankin gwaje gwaje na IS, gungun dabarun musammun biyar na IS, da kuma wasu sansanonin fakewar yaki biyar na IS.

Haka kuma, dakarun gamayyar kasa da kasa sun kai hare hare ta sama sau 26 kusa da Al Asad, Kirkout, Hit, Al Qaim, Mahkmour, Sinjar da Tal Afar dake kasar Iraki, tare da lalata manyan gungun dakarun yaki hudu na IS, gungun dabarun musammun goma sha biyar na IS, sansanonin fakewar yaki tara na mayakan IS, yankunan gwaje gwaje biyu na IS, motoci takwas na IS, manyan gine ginen kungiyar guda uku, tankin yaki guda da wani kwantenan ruwa mallakar IS. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China