A jiya ne, bangaren sojan kasar Jordan ya tabbatar da cewa, kungiyar IS ta kashe matukin jirgin sama dan kasar mai suna al- Kasasbeh da ta yi garkuwa da shi, bangaren soja na kasar Jordan ya ce, zai mayar da martani mai karfi ga wannan lamari.
Bayan da aka samu labarin kisan al- Kasasbeh, sarki Abdullah na II na kasar Jordan dake ziyara a kasar Amurka ya dakatar da ziyarar tasa bayan da ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Amurka Barack Obama inda ya koma gida.
Ana zargin Sajida al-Rishawi da hannu a hare-haren kunar bakin wake da aka kai cibiyar ciniki ta kasar Jordan dake birnin Amman, inda fiye da mutane 60 suka mutu. (Zainab)