in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da kisan 'yan kasar Japan
2015-02-01 17:00:45 cri

Kungiyar IS ta gabatar da wani bidiyo kisan wani dan kasar Japan Kenji Goto, game da hakan babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi tir da allawadai wannan kisa da IS ta yi a ran 31 ga watan Jarairu da ya gabata, tare da yin kira ga IS da dai sauran kungiyoyin ta'addanci da su sako mutanen da suke garkuwa dasu ba tare da wani sharadi ba.

Kakakin mista Ban ya ba da wata sanarwa a wannan rana da dare cewa, da babbar murya mista Ban ya yi Allah wadai da wannan laifi maras imani, tare da jajantawa gwamantin kasar Japan da jama'arta.

A cikin wannan sanarwa, mista Ban ya jaddada cewa, kisan Kenji Goto lamari ne dake nuna cewa, har yanzu ana fama da karfin tuwo a Iraqi da Sham. Ya sake yin kira ga IS da dai sauransu kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi da su saki dukkanin mutane da suke garkuwa da su.

Idan ba a manta ba, kungiyar IS ta gabatar da wannan bidiyo na kisan Kenji Goto a daddaren ran 31 ga watan Jarairu. Bidiyon ya nuna, wani dan ta'addan da fuskarsa take rufe ya yiwa Kenji Goto yankan rago, tare kuma da barazanar kara kashe 'yan kasar Japan nan gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China