A safiyar Lahadi ran 1 ga watan Fabrairu Kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ta gabatar da wani bidiyo game da kisan wani dan kasar Japan Kenji Goto da ta yi, lamarin da ya janyo bacin ran gwamnatin kasar Japan sosai.
Firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya ba da sanarwa a baya baya cewa, Japan ba za ta mika wuya ba ga ta'addanci, kuma za ta ci gaba da bada tallafin jin kai a yankin Gabas ta tsakiya.
A ran 20 ga watan Janairun da ya gabata, kungiyar IS ta gabatar da wani bidiyo, inda ta nemi Japan da ta biya dala miliyan 200 cikin sa'o'i 72, idan ba haka ba, za ta kashe 'yan kasarta biyu da ta kama wato Kenji Goto da Haruna Yukawa. Daga baya kuma, shafin yanar gizo na Intanet na kungiyar IS ya gabatar da wasu hotuna da bayanai dake nuna cewa, ta riga ta kashe Haruna Yukawa a ran 25 ga watan Jarairu, kuma a ran 27 ga wannan wata, IS ta gabatar da wani bidiyo na Kenji Goto inda ta yi barzana cewa, sa'o'i 24 kawai ya rage. (Amina)