Sanarwar ta bayyana cewa, wannan kisa ya kasance a matsayin wani kashedi gare mu cewa, 'yan jarida dake kasar Syria suna fuskantar hadari sosai, kana ya shaida cewa, kungiyar IS tana kawo babbar illa ga tsaron kasar Syria da jama'ar kasar Iraki, tilas ne a dauki matakai da yanke hukunci kan kungiyar IS, kana ya yi kira ga kasa da kasa da gwamnatin kasar Japan da su yi hadin gwiwa kan wannan batu.
An fitar da bidiyo dake nuna kisan dan kasar Japan mai suna Kenji Goto a kan internet a daren ranar 31 ga watan Janairu. Bisa bidiyon, wani mutum da ya rufe fuskarsa ya yiwa Kenji Goto yankan rago, kana ya bayyana cewa, kungiyar IS za ta ci gaba da kashe 'yan kasar Japan. (Zainab)