Wani rahoton gidan talabijin na al-Mayadeen ya ce kungiyar IS zata yi musayar dan kasar Japan da wani matukin jirgin saman kasar Jordan da ta kama idan Jordan ta mika mata matar mai suna Sajida al-Rishawi.
Rahotannin sun ce kungiyar IS na sa ran ganin Jordan ta saki matar wacce aka tsare a gidan kaso na Jordan bayan da ta taka rawa a wani harin kunar bakin wake a Amman a watan Nawumbar shekarar 2005, to amma daga baya sai ta tsira da ranta bayan bam din da ta yi damara da shi ya ki tashi.
Daga baya gwamnatin Jordan ta kama matar kuma wata kotun soji ta yanke mata hukuncin kisa a watan satumbar shekarar 2006, to amma matar ta daukaka kara har sau biyu.(Suwaiba)