in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya nemi a yi amfani da makamashin nukiliya lami lafiya
2015-01-15 20:34:14 cri
A yayin da ake murnar cika shekaru 60 da bunkasa masana'antun nukiliya a nan kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta wani muhimmin bayani, inda ya yaba da sakamakon da masana'antun kasar Sin suka samu, kuma ya nuna yadda za a bunkasa masana'antun nukiliya a nan gaba bisa sabon yanayin da ake ciki yanzu.

Xi Jinping ya nuna cewa, a cikin shekaru 60 da suka gabata, ma'aikatan masana'antun nukiliya na zuriyoyi da dama sun bayar da gudummawarsu matuka wajen bunkasa masana'antun nukiliya da babu shi a da a nan kasar Sin. Sakamakon gudummawar da suka bayar, yanzu masana'antun nukiliya na kasar Sin sun samu ci gaban dake jawo hankulan duniya sosai, har ma yana taka rawa kwarai ga ci gaban tattalin arziki da tabbatar da tsaron kasar gaba daya.

Xi Jinping ya kara da cewa, masana'antun nukiliya muhimman masana'antun zamani ne, kuma su ne muhimmin ginshikin tsaron kasar. Sabo da haka, Xi Jinping ya bukaci a tsaya tsayin daka kan matsayin kirkiro sabbin fasahohin bunkasa masana'antar lami lafiya, sannan ya kamata a yi amfani da makamashin nukiliya cikin lumana. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China