in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da kungiyar CELAC za su fidda tsarin hadin giwa na shekaru 5 in ji shugaba Xi
2015-01-08 15:24:52 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce kasarsa da kungiyar kasashen Latin Amurka da Caribbean ko CELAC a takaice, za su fayyace cikakkun bayanai game da tsarin hadin gwiwarsu na shekaru biyar masu zuwa.

Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan yayin jawabin bude dandalin tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, ya kara da cewa, tsarin hadin gwiwar ya kunshi yarjejeniyar birnin Beijing, da kuma ka'idojin hadin gwiwar Sin da kungiyar CELAC, matakin da zai zamo ginshikin taron ministocin bangarorin biyu.

Ya ce yarjejeniyar birnin Beijing za ta kunshi dukkanin batutunan siyasa da aka cimma ra'ayi guda a kansu, tare da saita alkiblar dandalin hadin gwiwar, da kuma fayyace ka'idodjin hadin kai.

A daya hannun kuma, babban tsarin hadin gwiwar zai kunshi bayanai game da muhimman sassa, da kuma matakai na musamman, da za su jagoranci hadin gwiwar bangarorin, tun daga bana, ya zuwa shekarar 2019 mai zuwa.

Shugaba Xi ya ce wadannan tsare-tsare na kunshe da manufofin hadin kan Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean, a fannin siyasa, da tsaro, da cinikayya, da zuba jari da harkokin hada-hadar kudade. Sauran sun hada da fannin makamashi, da samar da ababen more rayuwa, noma da bunkasa albarkatu da masana'antu, kimiyya, da kuma musayar fasahohi tsakanin al'ummun sassan biyu.

Daga nan sai shugaba Xi ya jaddada burin kasar sa, na bunkasa wannan hadin gwiwa, ta yadda zai kai ga samar da kudaden cinikayya, da za su kai dalar Amurka miliyan dubu 500 cikin shekaru 10 masu zuwa. Yayin da Sin ke fatan shigar da jarin da zai kai dalar Amurka miliyan dubu 250, cikin tsare-tsaren hadin gwiwar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China