in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jajantawa takwaransa na Mozambique bisa bala'in ambaliyar ruwa
2015-01-28 11:07:16 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bugawa takwaransa na kasar Mozambique Filipe Nyusi wayar tarho, inda ya gabatar masa da ta'azziya da jaje, bisa aukuwar bala'in ambaliyar ruwa a kasar ta Mozambique.

Mr. Xi ya gabatar da sakon jajen ne a madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, ya na mai bayyana alhinin sa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan bala'i.

Ban da haka kuma, Mr Xi ya ce, Sin na fatan samar da taimako ga Mozambique, tare da imanin cewa, jama'ar kasar za su tinkari wannan bala'i, su kuma cimma nasarar maido da gidajensu, karkashin jagorancin shugabannin gwamnatin kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China