An buga wani littafi mai dauke da zababbun kalamai na shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ya yi a kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma fafutuka na samar da tsarkakkiyar jam'iyyar 'yan kwaminis ta kasar Sin.
Littafin wanda aka rarraba shi gida tara yana kunshe da kalamai 216, da Xi ya yi daga cikin bayanai 40 da ya gabatar tsakanin ranar 15 ga watan Nawumba na shekarara 2012 zuwa 23 ga watan Oktoba na shekarar ta 2014.
Wata sanarwa wace bangaren yada labarai na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC ta gabatar ta ce, yawancin kalaman an wallafe su ne a karon farko, kuma sanarwar ta bukaci jami'an gwamnati, 'yan jam'iyyar CPC da su yi koyi da kalaman dake cikin littafin domin tunkarar matsalar cin hanci da rashawa. (Suwaiba)