Kwamitin wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwar da aka ba da a karshen cikakken zama na 5 na kwamitin ladabtarwa na JKS karo na 18 da ya gudana daga ranakun Litinin zuwa Laraba a nan birnin Beijing, ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar a dauki matakai na siyasa, da nuna juriya wajen kawar da wannan matsala.
Bugu da kari sanarwar ta ce, muddin ana bukatar a kawar da matsalar cin hanci, akwai bukatar jama'a su ba da goyon baya tare da shiga a dama da su sosai har ma da kafofin watsa labarai.
Sanarwar ta kuma yi kira ga dukkan kwamitoci na JKS a dukkan matakai da su kara daura damara a wannan yaki.
A shekarar da ta gabata ce aka sake nazarin aikin da ake kan yaki da cin hanci inda aka bayyana cewa, an cimma nasarori da dama a karkashin shugabancin JKS, kokarin dukkan hukumomi da mambobin jam'iyya gami da goyon bayan jama'a da kuma aikin tukuru na sipetocin ladabtarwa. (Ibrahim Yaya)