Shugaban kasar Sin Xi Jinping isar da sako ga sabon sarkin Saudiyya Salman bIn Abdul-Aziz al Saud don mika ta'aziyya ga rasuwar tsohon sarki Abdullah Bin Abdal-Aziz. A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, shugaba Xi ya bayyana matukar bakin ciki, tare da gai da sarki Salman, gwamnati da jama'a na kasar ta Saudiyya. Shugaba Xi kuma ya bayyana cewa, sarki Abdullah Bin Abdal-Aziz wani fitaccen sarki ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin inganta cigaban kasa da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya. Kuma shi aminin kasar Sin, wanda ya mai da hankali a kan ingiza dangantakar sada zumunci tsakanin kasar Saudi Arabiya da Sin, ya bayar da gudunmuwa kwarai wajen zurfafa wannan zumunci da hadin gwiwwa. Rasuwar tsohon sarki ba ma kawai babban rashin ga jama'ar Saudiya ba, kuma ya yi wa Sin hasarar wani sahihin amininta, hakan ya sa shugaban Xi yana matukar bakin ciki. (Amina)