Cikin sakon, shugaba Xi ya ce, tun lokacin da cutar Ebola ta barke a wasu kasashen yammacin Afirka, tawagogin ma'aikatan lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasashen da abin ya shafa suka dukufa tare da jama'ar wadannan kasashe wajen yaki da cutar, inda suka sami sakamako mai gamsarwa kan ayyukan jinya, ba da horo game da harkokin yin rigakafi da na kiwon lafiya da dai sauransu.
Lamarin ba kawai ya nuna zumuncin dake tsakanin jama'ar Sin da Afirka ba, haka kuma ya sa kasar Sin ta samu yabo daga gwamnatocin kasashen da abin ya shafa da al'ummominsu, har ma da gamayyar kasa da kasa.
Bugu da kari, shugaba Xi Jinping ya bayyana fatan cewa, ma'aikatan lafiyar za su ci gaba da dukufa kan wannan aiki, har lokacin da za a kawo karshen yaduwar cutar a kasashen, za su kuma ba da sabuwar gudummawa ga zumuncin Sin da Afirka, haka kuma, dukkanin jama'ar kasar Sin na jiran komawarsu gida cikin nasara. (Maryam)