Shugaban ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar na murnar shiga sabuwar shekara da aka watsa ta kafofin watsa labaran kasar, inda ya shaidawa jama'a a ciki da wajen kasar cewa, ba za a taba mantawa da shekara ta 2014 ba.
Ya ce, a shekara ta 2014 an aiwatar da gyare-gyare da dama, warware wasu matsaloli baya ga wasu muhimman matakan yin gyare-gyare wadanda suka dace da marudun jama'ar kasar.
Shugaban ya kuma yaba da irin gudumawar da dukkan rukunonin ma'aikata suka bayar, shugaban ya ce, ba don su ba, ba za a cimma nasarar da aka samu a yanzu ba.
Xi ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka da nufin kare 'yanci da muradun jama'a, tare da ba da tabbaci ga jin dadin rayuwa da ci gaban kasar.
Daga karshe shugaba Xi ya ce, wajibi ne a ci gaba da tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka ta yadda za a samu cikakkiyar al'umma mai wadata ya zuwa shekara 2020 kamar yadda aka tsara. (Ibrahim)