in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin Xi Jinping ya jajantawa iyalan mutanen da suka rasu sakamakon hadarin jirgin saman kamfanin AirAsia
2014-12-31 10:05:08 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Indonesia Joko Widodo a jiya Talata, inda ya bayyana ta'aziyyarsa game da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin saman kamfanin AirAsia.

Xi Jinping ya bayyana cewa, hadarin jirgin na kasar Indonesia ya tayar da hankanlin sa matuka, ganin yadda hadarin ya haddasa mutuwar mutane da dama, ciki har da fasinjoji daga kasar Indonesia.

A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, shugaba Xi ya bayyana alhini game da asarar rayukan da aka samu sakamakon hadarin, ya kuma jajantawa iyalan wadanda hadarin ya ritsa da su. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China