Jami'in na AU ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai na kasar Sin a Addis Ababa,babban birnin kasar Habasha,inda ya yaba da irin rawar da kasar Sin ke takawa ga ci gaban tattalin arzikin Afirka a cikin shekarun da suka gabata,musamman yadda kasar ta Sin ke bukatar kayayyakin nahiyar.
Mwencha ya ce,Sin da Afirka na tattaunawa don kara inganta dangantakar da ke tsakanin su a fannoni daban-baban ta hanyar dandalin nan na hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCA). (Ibrahim)