Shugaban kwamitin tsaron MDD a wannan karo, zaunannen wakilin kasar Rasha dake MDD Vitaly Churkin da shugaban kwamitin zaman lafiya na kungiyar AU na wanna karo, zaunannen wakilin kasar Uganda dake kungiyar AU Mull Sbujja Katende sun gana da kafofin watsa labarai cikin hadin gwiwa bayan taron.
Yayin da suka yi tsokaci kan 'yan matan da aka yi garkuwa da su a kasar Najeriya, Mr. Katende ya bayyana cewa, kasashen kungiyar AU na ci gaba da neman wadannan 'yan mata cikin sirri. Shugabannin kasashen kungiyar AU dukkansu sun samar da taimako ga gwamnatin kasar Najeriya, kuma wasu na ci gaba da ba da taimako ga gwamnatin kasar domin ceto wadannan 'yan mata cikin sauri.
Bugu da kari, Mr. Katende ya kara da cewa, kungiyar AU na mai da hankali sosai kan yin hadin gwiwa yadda ya kamata da MDD wajen yaki da ta'addanci, kuma tana son ci gaba da karfafa musayar labaran yaki da ta'addanci dake tsakanin bangarorin biyu a nan gaba. (Maryam)