in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin kungiyar AU karo na 23
2014-06-20 15:46:11 cri
A ranar 20 ga watan Yuni da safe ne an bude taron kolin kungiyar AU karo na 23 a birnin Malabo dake jamhuriyyar Equatorial Guinea, bisa taken "aikin gona, tsaron abinci da kuma kyautata tsarin aikin gona na Afirka: amfani da dama don samun bunkasuwa mai dorewa ba tare da yin la'akari da bambance-bambance ba".

Za a shafe kwanaki 8 ana gudanar da taron kolin. Kuma a ranakun 26 da 27 ga wata, za a yi babban taron shugabannin kasashe membobin kungiyar ta AU, wanda ya kasance muhimmin bangare a yayin taron kolin. Inda ake fatan tattauna wasu batutuwa a gun taron kolin, ciki har da kara samar da amfanin gona, kara karfin aikin gona da muhimmancin amfanin gona, inganta kasuwa da ciniki a fannin aikin gona, kawo karshen matsalar yunwa a nahiyar Afirka kafin shekarar 2025, kara zuba jari a bangaren aikin gona da dai sauransu.

Game da batun aikin gona da tsaron abinci, za a gudanar da dandalin tattaunawa na aikin gona na nahiyar Afirka, inda za a tattauna kan manyan matsaloli da ake fuskanta a wannan fanni, da sa kaimi da cika alkawarun da aka dauka, da kuma gaggauta kyautata tsarin aikin gona ta hanyar samun bunkasuwa ba tare da yin la'akari da bambance-bambance ba, da kuma sa kamfanoni masu zaman kansu su zuba jari ga aikin gona. Hakazalika kuma za a gudanar da wani taron tattaunawa game da sa kaimi ga mata da su shiga aikin inganta aikin gona, tsaron abinci da fa'idojin da ake samu a bangaren aikin gona, ana sa ran cewa, mata fiye da 60 da suka zo daga kasashen Afirka za su halarci taron. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China