in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar kungiyar AU ta yi kira ga kasashen Afirka da su kara goyon baya ga aikin gona
2014-06-25 14:12:11 cri
A gun taron kungiyar AU dake gudana a birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea, Jami'a mai kula da harkokin tattalin arziki na kauyuka da aikin gona na kwamitin kungiyar AU Rhoda Peace Tumusiime ta yi kira ga kasashen Afirka da su kara goyon baya ga aikin gona a fannonin manufofi da kudi.

Madam Rhoda ta bayyana cewa, kasashen Afirka sun riga sun cimma daidaito kan kyautata tsarin aikin gona don tabbatar da samar da isashen hatsi da warware matsalar yunwa.

Hakazalika, Rhoda ta yi kira ga kasashen Afirka da su kara hadin gwiwa wajen saye-sayen kayayyaki a yankin Afirka, da bunkasa fasahohin aikin gona da kuma tabbatar da samar da isashen hatsi a Afirka.

Shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, za su gaggauta yin kwaskwarima kan harkokin aikin gona, da gabatar da wani shiri a wannan mako don tabbatar da burin kawar da yunwa kafin shekarar 2025. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China