Al-Sisi ya ce, kasar Masar tana kokarin yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen Afirka don inganta karfin Afirka a fannonin magance rikicin diplomasiya, tashe-tashen hankali da ta'addanci ta yadda ake iyar sake gina da bunkasa kasashen bayan rikici.
Hakazalika kuma shugaban Masar ya kara da cewa, game da barazanar da ta'addanci ke kawo wa kasa da kasa, tilas ne kasashen Afirka su tsaya tsayin daka kan yin tir da duk wani nau'in ta'addanci, da kara yin hadin gwiwa, da sa kaimi ga kasa da kasa wajen kara yaki da ta'addanci domin tabbatar da tsaron fararen hula da bunkasa tattalin arzikinsu. (Zainab)