Shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta yi wani jawabi a gun bikin kaddamarwar taron, inda ta yi kira ga kasashen Afirka da su kafa tsarin aikin gona na zamani, kirkiro sabbin fasahohin aikin gona da kuma inganta sha'anin sarrafa amfanin gona.
A gun taron, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ana samun zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arziki a yawancin kasashen Afirka, kuma an samu ci gaba yayin da ake yin kokarin cimma burin muradun karni na MDD. Kana yayin da ake kokarin cimma burin shekarar 2063 a Afirka, MDD tana son yin hadin gwiwa tare da kungiyar AU don sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa mai dorewa a Afirka. (Zainab)