Mista N'Guesso ya ce, game da sace 'yan mata fiye da 200 da kungiyar ta yi, lokaci ya yi ga Afrika data dauki tsaurarrun matakai da kanta. A ganinsa, koda yake yana goyon bayan taimakon gamayyar kasa da kasa, amma duk da haka wannan batu ne da ya shafi Afrika.
Kan batun Najeriya, rikicin Sudan ta Kudu da Afrika ta Tsakiya, wadannan batutuwan Afrika ne kuma ya kamata a ce Afrika na sahun gaba wajen warware matsalolinta in ji shugaban kasar Congo, da yake jawabi a yayin taron kasashen Afrika goma na tarayyar Afrika AU kan kawo gyaran fuska ga kwamitin sulhu na MDD da ya gudana a ranar Jumma'a a birnin Oyo mai tazarar kilomita 400 daga birnin Brazzaville.
Shugaban kasar Congo ya kara da cewa,Afrika na daukar makomarta ga hannu. Abin da kasashen Afirka suke kokarin yi ne bisa karfinsu a nan tsakiyar nahiyar Afrika musammun ma kan batun da ya shafi Afrika ta Tsakiya. Akwai akalla sojojin wanzar da zaman lafiya na shiyyar Afrika fiye da dubu shida dake kasar Afrika ta Tsakiya. Don haka ana tunanin kafin a yi jiran taimako daga wajen gamayyar kasa da kasa, ya kamata Afrika ta fara daukar matakinta bisa 'yanci A nata bangare.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Senegal, Mankeur Ndiaye ya bayyana cewa ana allawadai da abubuwan da suka faru a tarayyar Najeriya. (Maman Ada)