Wurare daban-daban na kasar Afrika ta kudu sun yi bukukuwa iri daban-daban a ran 1 ga wata domin tunawa da ranar kasa da kasa kan masu fama da cutar Sida karo na 26, inda gwamnatin kasar ta yi kira ga jama'arta da su shiga aikin yin rigakafi da ba da jiyya ga mutanen dake fama da wannan cuta, ta yadda za a cimma burin na hana karin mutane kamuwa da wannan annoba.
A wani taron da aka yi a wannan rana a lardin Mpumalanga, mataimakin shugaban kasar Kgalema Petrus Motlanthe ya yi kira ga jama'a da su amince da binciken jininsu, ta yadda za a gano wadanda suke dauke da kwayoyin cutar kanjamau tun da wuri, da hana yaduwar cutar. Yana mai cewa, abin da ya kasance babban mataki wajen yin rigakafi da ba da jiyya ga masu fama da cutar.
Tun lokacin da shugaban kasar Jacob Zuma ya kaddamar da aikin bincike jini a shekarar 2010, ya zuwa yanzu, an yi bincike ga mutane kimanin miliyan 20. Burin gwamnatin kasar shi ne, na gudanar da bincike ga kowane mutan kasar a kalla sau daya a kowace shekara daga shekarar 2012 har zuwa 2016. (Amina)