Shugaba Xi Jinping ya isa yankin Macau ne domin halartar bikin taya murnar cika shekaru 15 da komawar yankin Macau a karkashin kasar Sin kuma bikin rantsuwar kama aikin gwamnatin yankin karo na 4.
Xi Jinping ya bayyana cewa, ya ji farin ciki da sake kai ziyara a yankin Macau bayan shekaru biyar. Burinsa a ziyarar wannan karo shi ne taya murnar ranar komawar yankin Macau a kasar Sin tare da mazauna yankin tare, da isar da gaisuwa daga gwamnatin tsakiyar kasar Sin da sauran al'ummomin kasar ga mutanen yankin.
Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya ce, zai gana da jama'ar dake yankin, da kuma waiwayi tarihin yankin na tsawon shekaru 15 bayan da yankin ya koma karkashin kasar Sin, da tattauna hanyar samun bunkasuwa a nan gaba. (Zainab)