A lokacin ganawar Mr Zhang ya bayyana cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na fatan sa kaimi ga kafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin ta da majalisar dokokin kasar Senegal na lokaci mai tsawo domin karfafa hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki, cinikayya, al'adun bil'adam da sauransu, ta yadda za'a tabbatar da bunkasuwar dangantaka a tsakaninsu lami lafiya kuma bisa tsari.
A nasa bangare, shugaba Macky Sall ya bayyana cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a fannin siyasa kuma ya yi imani cewa, bisa goyon bayan majalisun dokokin kasashen biyu, dangantaka tsakanin Sin da Senegal za ta bunkasa cikin sauri yadda ya kamata.(Fatima)