A jiya Talata 18 ga wata ne, aka gudanar da bikin mika kayayyakin a makarantar sakandare ta Ndiar dake da nisan kilomita 60 daga babban birnin kasar, Dakar.
A shekarar 2009 ne aka kammala gina makarantar, wadda kasar Sin ta ba da taimako wajen gina ta, a halin yanzu, wannan makaranta na da dalibai guda 286 da kuma malamai guda 16.
A shekarar 2013, jakadan kasar Sin dake kasar Senegal ya taba samar wa makarantan na'urar kwanfuta, na'urorin nuna hotunan bidiyo da litattafai da sauran kayayyakin karatu da na motsa jiki. (Maryam)