Mr Li ya bayyana cewa, bayan bunkasuwar dangantaka da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin shekaru 50 da suka wuce, yanzu ana cikin yanayi mai kyau cikin adalci da moriyar juna da yin hakuri a bangarorin biyu.
A cikin wannan sabon yanayi kuma, inji Firaministan yace kasar Sin ta kara yin kwaskwarima a duk fannoni tare da kara bude kofa ga kasashen waje abinda zai kawo sabon zarafi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.
A nasa bangare shi ma, shugaba Macky Sall ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, dangantaka tsakanin Senegal da Sin ta sami ci gaba kwarai da gasket kuma gudummawar da Sin ta bayar ta sa kaimi ga bunkasuwar Senegal sosai.(Fatima)