in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi allah-wadai da tashin hankalin da ke faruwa a Masar
2014-01-27 21:18:39 cri
A yau Litinin ne kasar Sin ta yi allah-wadai da hare-haren da ake kaiwa fararen hula da gine-ginen gwamnati a Masar, inda ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su hau kan teburin sulhu don kaucewa zubar da jini.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ne ya bayyana hakan, sakamakon tashin hankalin da ya barke ranar Asabar a kasar, yayin da Misirawa ke bikin cika shekaru 3 da juyin-juya halin da ya kai ga tumbuke gwamnatin Hosni Mubarak.

Ya ce kasar Sin tana fatan za a hanzarta mai do da doka da oda a kasar ta Masar, mika mulki yadda ya kamata ta yadda za a samu zaman lafiya da ci gaban kasa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China